ABNA24 : A lokacin da yake zantawa da manema labarai yau a birnin Tehran, Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh ya bayyana cewa, akwai ci gaba a tattaunawar da ke gudana a birnin Vienna, amma Iran tana taka-tsantsan matuka, domin akwai wasu batutuwa masu matukar muhimmanci da ba a riga an cimma matsaya a kansu ba.
Ya ce babban abin da Iran din take jaddadawa shi ne, komawarta zuwa ga yin aiki da bangarorin yarjejeniyar nukiliya da ta jingine, ya dogara da janye mata dukkanin takunkuman da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kakaba mata.
Dangane da batun dawo da kyakkyawar alaka tsakanin Iran da saudiyya kuwa, Khatib Zadeh ya bayyana cewa, akwai ci gaba a tattaunawar da ke gudana tsakanin Iran da Saudiyya, amma ba zai bayyana komai kan haka ga manema labarai ba a halin yanzu, har sai an cimma matsaya kan batutuwa da bangarorion na Saudiyya da Iran suke attatunawa a kansu.
342/